Monday, 19 November 2018
Wadanne Abubuwa Ake So Mace Ta Fi Mijinta Da Su?

Home Wadanne Abubuwa Ake So Mace Ta Fi Mijinta Da Su?

Assalamu alaikum. Wasu tambayoyi nake rokon Malam da ya taimakamin da
amsoshinsu in Allah ya sa malam ya sansu. 1.Shin akwai wasu abubuwa uku da ake so mata tafi mijin da za ta aura da su, sannan shi ma akwai abu guda uku da ake so ya fita da su? Kuma ko akwai wadanda suka yi musharaka a kansu? Da fatan Malam ya san su kuma za a taimaka min da su. Na gode.

To dan’unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku: ta fi shi a kyau, ta fi shi kananan shekaru, ta fi son shi sama da yadda yake sonta. Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta. Ana so su hadu a abubuwa uku: ya zama akwai yaren da yake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za’a samu jin dadin aure.

Don neman karin bayani ka nemi shirin da na yi a Freedom Radio kano, ranar : 3 ga Ramadhan 1434 hi, a shirinsu na Minbarin Malamai

Na Sha Nonon Matata, Yaya Auranmu?
Don Allah Malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake?
To dan’uwa Allah Madaukakin Sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan

bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila, don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu:

Ya Halatta. saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi S.A.W “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha

saboda yunwa”, Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

Bai Halatta ya sha ba. saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi S.A.W ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, sai dai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau.

Don neman Karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 2\67. Allah ne mafi sani

Share this


Author: verified_user

0 Comments: