Friday, 16 November 2018
Karanta Kaji Halayen Maza Guda Biyar (5) Da Suke Birge Mata

Home Karanta Kaji Halayen Maza Guda Biyar (5) Da Suke Birge Mata
A dai-dai lakacin da mata suke bukatar abubuwa a wajen maza domin gudanar da kyakkyawan zamantakewa, ga kadan daga cikin su:

Halaye guda biyar da mata suke sha’awa kuma su birge su a wajen maza wadanda bas u shafi surar jikinsu ba.
Akwai wasu halaye da kuma yadda kake gudanar da harkokinka da za su kara manaka kwar jinni wajen masoyanka.
Ka manta da wasu kyalekyalen da babu amfani, maimakon haka ka lizimci halayen da mata zasu yi sha’awar magana da kai da son kasancewa da kai, in ka shirya sanin wadannan halaye, to ka saurara.

1. Yarda da kai:
Mata mutane ne kamar maza suna da tabbaci kuma suka yarda da kansu. Namijin da bashi da tsayuwar yanke hukunci, ya kan sa mace cikin rashin tabbas, dole nauyin yanke hukunci ya kasance a kan namiji, rashin karfin gwiwar yanke hukunci ga namiji yana karya kwarin gwiwar mace, ta ji kamar ba ta da mai kare ta musamman in sun fita zuwa wani sha’ani.

2. Tausayi:
A kwaikwai banbanci tsakanin samun kwarin gwiwa da kuma kasancewa mutumin da bashi da tausayi da sausauci, haka abin yake ko a harkokin kasuwanci ne ko kuma a hulda tsakanin mace da namiji, yana da matukar mahimmanci kada ka zama mai kokarin rusa wani don ka daukaka kanka. Dagawa yana kasacewa barazana ne ga wadanda suke kusa da kai.

3. Kyakkyawan Zato:
Kyautata zaton faruwar alhairi a duk al’amuran da ka fustanta ba daya yake da lamarin samun kwarin gwiwa ba, a matsayinka na namiji dole ya zamana kana da karfin gwiwa da kyakyawan zaton faruwar lamari koda kuwa mutane na ganin lamarin nada tsananin wahala. Mata na matukar sha’awar mai irin wannan halayen.

4. Girmamawa:
Mata na matukar jin dadi yayin da namiji ya bude musu kofa ko kuma ya ba su wajen zama, amma mafi mahimmaci, suna son maniji ya nemi ra’ayinsu a kan wani lamari, suna kuma matukar sha’awar namiji da yake taimakon wasu.

5. Ka zama mai sauraron matsalolinsu:
Mata na matukar son a tattauna matsalolin daya shafesu, haka kuma mata sun fi sha’awar namijin da yake sauraron bukatunsu ya kuma kasance baya mantawa da abin da ta fada masa, to tabbas masu irin wadannan halayen za su zama ‘yan lelen mata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: