Wednesday, 14 November 2018
Kannywood: Yan Sanda Sun Kama Bindigogi A Gidan Ali Nuhu

Home Kannywood: Yan Sanda Sun Kama Bindigogi A Gidan Ali Nuhu
Yan Sanda Sun Kama Bindigogi A Gidan Ali Nuhu

Nasan wannan hoton da kuka gani zai razana ku sosai na ganin yan sanda tare da jarumi Ali Nuhu da miyagun makamai haka a gabansu wanda hakan ka iya kawo muku tunanin cewa ko an kama shi ne dasu.

Shidai wannan hoto da kuke gani an dauke shine a yayin da ake daukar wani film ( kamar Film din Ana Muslim ) , inda a ciki shi jarumi Ali Nuhun ya hau wannan matakivna wanda aka samu makamai a gidansa..

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan hoto da sarki Ali Nuhun ya dora a shafinsa na Facebook inda wasu daga ciki suka bada shawarar cewa bai kamata ya dora wannan hoto ba don kada wasu su dauka ko da gaske ne, a yayin da wasu kuma suke ganin hakan ba wani illa bane.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: