Monday, 19 November 2018
Ga Sabbin Amare: Sirrin Rike Miji…..(Ki karanta don karin Ilimi)

Home Ga Sabbin Amare: Sirrin Rike Miji…..(Ki karanta don karin Ilimi)


Mallakar miji da rarrashin miji yayin fushinsa yana daga tabbacin samun zaman lafiya a cikin fushi ko kika Saba masa ki yi gaggawar nadama da ba shi hakuri kamar kice;

“Kayi hakuri masoyi , ban san ranka zai baci ba” ko kuma “Allah ya huci zuciyar ka ka yafe min, in baka yafe min ba ba Zan samu natsuwa ba” da dai sauran maganganu na kwantar wa da maigida hankali da sanyaya zuciya.

Kada ki kuskura ki saurari wasuwasin shaidan ya Kai ki ya baro ki kasance mai tunowa da fadin ubangiji madaukakin sarki:

“kuma kace wa bayina, su fadi kalma wadda take mafi kyau. lallai ne shaidan yana sanya barna a tsakaninsu ” ( al’isra ‘i 53)

ki kasance mai sakin fuska da murmushi a gare shi, kada ki daga masa murya, ki zama mai tausasa murya kada kuma ki mayar masa da martani da kakkausar magana a lokacin fushinsa, ki zama mai nadama da ban hakuri a gareshi, to wannan sai zuciyar sa ta sauko yaji yana kaunar ki da tausayi a gareki.

A hikimance akace : “fushin miji fushi ubangiji ne”.
A kace kuma: idan miji yayi fushi to mala’iku ma sun yi fushi.
SON ABINDA MIJI YAKE SO

yana da kyau ‘yar’uwa yayin da kika zauna da mijinki kiyi gaggawa fahimtar dabi’unsa da fahimtar wane abune mijinki yake so kuma wane abune Wanda baya so, ki nuna kinfi shi son abin fiye da shi, ko da ke ba kya so ki jurarwa zuciyar ki a kan son abin matukar ba sabon Allah bane.
○SIRRINKA NA MUSANMAN○
Sirrin rike miji

BUSHEWAR JIKI

‘Yar’uwa kada ki bar jikinki ya rika bushewa da yaushi ba jini a jikinki. ki zama mai taushin fata da laushin fata kamar auduga sirrin shine a samu wadannan mahadan:

Karanta wannan: Jami’an NSCDC Ta Cafke Wasu Masu Garkuwa Da Mutane A Neja

✪ zuma
✪ garin alkama
✪ kwanduwar kwai
✪ man zaitun
✪ ruwa

Da farko a samu zuma mai kyau sai a zuba ruwa tare da kwanduwar kwai danya da kuma garin alkama tare da man zaitun, sai a hada su waje daya a jujjuya a rikka shafe fatar jiki da shi.

HASKEN FATA

Da farko fatarki tayi haske da kyau to sai ki yi kokarin hada wannan sirrin da farko Zaki samu bawon lemon Zaki sai ki shanya shi ya bushe, idan ya bushe to sai ki nika shi ko ki daka shi yayi laushi to sai ki samu madarar shanu sai ki kwaba shi sannan sai ki shafa shi kullum da safe da yamma sai ki wanke da ruwan dumi to wannan hadin zai sa fatarki tayi kyau da haske.

MANTA KISHIYA

‘Yar’uwa wannan wani hadin ne na musamman in kina yin sa ya Bi jikinki to ni’imar da Zaki samu ba karrama bace.
zuma
Citta
Tufah
‘Ya’yan kankana

Da farko ki samu citta ya’yan kankana sai ki daka su yayi laushi, daga nan sai ki samu tufah (aful) kamar biyu ko uku sai ki markada ta, sai ki samu zuma ki mai kyau sai ki zuba a ciki tare da Rabin karamin cokali na garin citta, babban cokali na garin ya’yan kankana, sai ki zuba ki juya su sai a rikka shan babban cokali uku safe da yamma akoda yaushe.

MENENE SIRRIN?
Yar’uwa sirrin abune muhimmi a zamantakewar ta aure, ke dai kula da kanki da gyara jikinki a koda yaushe mahadan wannan sirrin shine;

– Nono
– Zuma
– Dabino

Da farko ki samu dabino mai kyau sai ki cire kwallon, sai ki sa dabino a cikin nono ki barshi ya jiku sai ki markada shi, sannan ki kawo zumarki mai kyau ki zuba a ciki sai ki rikka shan kofi daya da safe daya da yamma zuwa kwana (7) to hakika yar’uwa Zaki ga yadda Zaki rika naso na ni’ima a jikinki.

SIRRIN MALLAKAR MIJI
– Gyara jiki gyaran fata
– Gyara gashi
– Ruwan nono
– Magani ciwon nono
– Samun ni’ima
– Gyaran jiki amarya
– Cuwon Mara

Share this


Author: verified_user

0 Comments: