Sunday, 18 November 2018
Ahmed Musa Yayi Murna Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Nigeria

Home Ahmed Musa Yayi Murna Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Nigeria
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya ce ya yi matukar murnar lashe gasar gwarzon dan wasan kwallon kafar Najeriya na 2018.


A sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Asabar, dan wasan na kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya, ya ce lashe wannan gasa "ya sa na kaskantar da kaina."

"Godiya ga abokan wasana wadanda suka sanya nake inganta wasana da kuma godiya ga dukkan mutanen da suka taimaka min," in ji dan wasan.
Ahmed Musa ya doke dan wasan baya na Super Eagles Kenneth Omeruo da 'yar wasan Super Falcons Rasheedat Ajibade wadanda suka shiga gasar.

An sanya sunan kwallon da Ahmed Musa ya zura a wasan Najeriya da Iceland na gasar cin kofin duniya na 2018 a matsayin kwallon da ta fi kayatarwa.

Dan wasan shi ne dan Najeriya na farko da ya zura kwallo fiye da sau daya a gasar cin kofin duniya ta FIFA.
BBChausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: