Saturday, 20 October 2018
Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya

Home Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya
Ronaldo zai bar Juventus zuwa wata kungiya


Kwanannan ne Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus inda ya fara taka leda yanda ya kamata, duk da dai yanzu anata badakalar fyade da wata 'yar kasar Amurka tace ya mata, an ruwaito Ronaldo na da shirin barin Juve din.

Shafinnan na kasar Sifaniya daya saba kwarmato labaran sayar da 'yan wasa kuma mafi yawanci sukan zama gaskiya watau Don Balon ya kwarmato cewa tauraron dan kwallon Ronaldo zai sake tsayawa kakar wasa daya a Juventus.

Amma daga nan zai koma kungiyar kasar Amurka ta MLS Orlando da wasa inda zasu biyashi albashin miliyan 50 duk kakar wasa na tsawon shekaru 2 idan dai hakan ta tabbata to Ronaldon zai zama dan wasan da yafi kowane dan wasa karbar Albashi a Duniya.

Shafin ya kuma ruwaiyo cewa Ronaldon na da burin sayen hannin jari a kungiyar ta MLS bayan yayi ritaya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: