Friday, 21 September 2018
Karanta sabuwar dabararmar da masu kudi ke amfani da ita wajan yin lalata da mata: Sai ka rike baki

Home Karanta sabuwar dabararmar da masu kudi ke amfani da ita wajan yin lalata da mata: Sai ka rike baki
Karanta sabuwar dabararmar da masu kudi ke amfani da ita wajan yin lalata da mata: Sai ka rike baki

Duniya inda ranka zaka ji ka kuma ga abubuwan ban mamaki da yawa, a yayin da malamanmu ke ta kara jan hankalin mutane da a gujewa manyan laifuka, wasu kuwa kara fito da sabon salo suke na tsunduma cikin laifin ido rufe. Zina dai haramunce bama a addinin musulunci ba kadai, harma da sauran wasu addinai.

Duk musulmin kwarai kuwa zai guje mata. Wani lamari me kama da almarane ya faru da wata mata da wani mutum me aure ke son yin lalata da ita.

Baiwar Allahn ta dade tana rokon Allah ya tsareta daga aikata Zina, har taje aikin Hajji inda can ma ta roki Allah kada ya nuna mata ranar da zata aikata Zina, kwatsam sai ga mutumin wanda yana da mata ya sameta inda ya bayyana mata cewa shifa kawai bukatarshi yayi lalata da ita.

Ta gayamishi itafa ga irin addu'ar data ke yi ma akan neman tsari da yin Zina.

Yace mata, kar ta damu idan sukayi suka gama zai biya mata kudi ta sake komawa Makka dan ta roki Allah gafara, ko kumama suje can tare, idan suka gama sai suyi wanka su je dakin Allah su rokeshi gafara.

Shahararren me fadakarwa a shafin twitter, Mustafa da aka fi sani da Angryustaz ne ya bayar da wannan labari inda yace wadda abin ya faru da itane ta bashi labari.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: