Saturday, 21 July 2018
Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haifeta

Home Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haifeta
Karanta labarin jaririyar da aka dauketa aiki ranar da aka haife ta


Wata jaririya da aka haifa a jihar Texas ta kasar Amurka ta shigo Duniya da kafar dama inda ta samu aikin yi ranar da mahaifiyarta ta haifeta, iyayen wannan yarinya, Robert Griffin da mahaifiyarta,

Falon Griffin suna kan hanyarsune ta zuwa Asibiti sai Falon taji cewa tana bukatar shiga bandaki.

Mijin ya tsaya a kofar wani sananen gidan sayar da abinci me suna, Chick-Fil-A amma sun tashi aiki da yake cikin darene, haka dole ya kwankwasa musu suka bude, saboda matar tashi ta bayyana cewa abinda take ji, ba zata iya jira har sai sunje Asibitin ba, matar tashi ta shiga ban dakin gidan sayar da abincin.

Jiyo ihun Falon daga bandakin yasa Robert yayi gaggawar kaimata dauki, yana shiga sai yaga ai haihuwace zatayi, har kan jaririyar ya fara fitowa, kamar yanda ya bayyana a labarin daya bayar a shafinshi na Fcebook.

Robert yace ganin haka yasa ya tabbatar da cewa babu inda zasu iya zuwa daga nan, sai ya fara gaya mata maganganun kwarin gwiwa a haka har ta haihu a cikin bandakin, inda yayi amfani da rigarshi a matsayin zanin rike jaririyar, ya kuma lura cewa, cibiyar jaririyar ta nade mata wuya har sau biyu, anan ma yayi dabara a warware mata.

Ma'aikatan jiyya sun iso gurin daga baya sannan aka tafi da jaririyar da uwarta Asibiti, a wajan rubuta takardar haihuwarta, an rubuta sunan mahaifin nata Robert a matsayin wanda ya bayar da gudummuwa wajan haihuwarta.

Su kuwa gidan sayar da abincin wanda sanannene yayi alkawarin ba jaririyar abinci har tsawon rayuwarta sannan kuma da zarar takai shekaru 16 zai dauketa aiki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: