Thursday, 28 June 2018
Wai me yasa idan Namiji da mace suka je siyayya sai a rika tambayar namijin kudin kayan da suka siya? - Inji Nafisa Abdullahi

Home Wai me yasa idan Namiji da mace suka je siyayya sai a rika tambayar namijin kudin kayan da suka siya? - Inji Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana wani abu dake ci mata tuwo a kwarya, abin kuwa shine irin yanda idan mace da namiji suka je gurin siyayya sai a rika tambayar na mijin kudin kayan da suka siya.

Nafisar ta bayar da misalin zuwa siyayya da tayi tare da wani ma'aikacinta, tace, bayan sun kammala daukar abubuwan da zasu siya sai me shagon ya baiwa ma'aikacin nata takardar biyan kudi, tace, sai ta jira ma'aikacin nata ya miko mata takardar.

Bayan ya miko mata sai ta cewa me shagon to nice zan biya, Nafisa tace, me shagon yayi ta bata hakuri yace yana fatan bata ji haushi ba, ta gayamai cewa, taji kuma ya sani su mata suna iya ma kansu siyayya dama abinda yafi haka.

Ta kara da cewa idan taje kasar waje suka je siyayya da mutane ana tambayar sune mutum daya ne zai biya kudin kayan ko kuwa hadaka zasuyi?.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: