Friday, 8 June 2018
Rarara zai yi bayani kan zargin lamushe Naira miliyan 100

Home Rarara zai yi bayani kan zargin lamushe Naira miliyan 100

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa nan ba dadewa ba zai kira taron ’yan jarida don ya bayyana matsayinsa kan zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da kudin kungiyar mawakan Arewa kimanin Naira miliyan 100 da kungiyar Gwamnonin Arewa ta ba mawaka.

Mawakin ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa kuma manajansa, Al-ameen Afandaj a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Talatar da ta gabata.

Rarara ya ce nan ba dadewa ba zai kira taron kungiyar mawaka, sannan bayan taron zai gana da ’yan jarida don yi musu cikakken bayani dangane da hatsaniyar da ake yi kan batun kudin.

“A yanzu Rarara ba zai ce komai ba, sai bayan taron kungiyar mawaka, idan an sanya wurin da za a yi da kuma lokacin da za a yi, to zan gayyace ka, domin ka shaida komai a gabanka, kuma za a gayyaci manema labarai inda mawakin da kansa zai yi cikakken bayani a kan komai,” Inji shi.

Idan ba a manta ba dai jaridar Rariya ce ta fara kawo labarin batun zargin handame kudin da ake zargin mawaki Rarara da yi.

A cikin rahoton jaridar ta bayyana cewa kungiyar mawaka ta Arewa wato AMFO ta zargi mawakin da handame kudinsu kimanin Naira miliyan 100 da kungiyar Gwamnoni Arewa ta ba su.

Jaridar ta kara da cewa daya daga cikin mawakan da aka yi fadi tashi da shi wajen kare martabar Jam’iyyar APC, Abubakar Sani ya bayyana wa RARIYA cewa kusan mawaka 500 da suka bada gudummawa wajen nasarar gwamnatin APC, to wadanda suke amfana da gwamnatin ba su fi mutum biyu zuwa uku ba.

Jaridar ta ce, Abubakar Sani ya ce, “Idan ka duba da yawa daga cikin mawakan da aka yi wakar ‘Lema Ta Yage’ da su, duk sun dawo daga rakiyar Rarara saboda yadda yake amfani da sunansu yana bin manyan jiga-jigan APC yana karbar kudi.”

Abubakar Sani ya kara da cewa wani kuskure da aka samu kan badakalar kudin shi ne, rashin samar wa kungiyar asusun ajiya, inda Rarara ya rika amfani da asusun ajiyarsa wajen ajiye kudin.

Shugaban kungiyar mawakan Arewa, Haruna Aliyu Ningi da ke Jihar Bauchi ya bayyana wa manema labarai cewa, Gwamnan Jihar Zamfara ne ya ba su kudin bayan sun bukaci hakan sakamakon irin gudunmuwar da suka bayar a yayin zabukan 2015.

Jaridar ta rawaito cewa Aliyu Ningi ya ce, tun da farko Rarara ne ya shige gaba wajen karbo kudaden kuma, “ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara bayar da Naira miliyan 60, sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya ba su Naira miliyan 18.”

Ya kara da cewar, “A matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Rarara bai taba yi mini maganar ba, bayan lokacin da na sake tuntubar sa, sai ya ce har yanzu ba a cika ragowar kudaden ba, amma na kusa da shi wanda shi ma yana daga cikin mawaka, wato Isiyaku Oris ya ce tuni an ba Rarara ragowar Naira miliyan 40.”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: