Friday, 22 June 2018
Najeriya taci Iceland 2-0: Ahmad Musa ya kafa tarihin zama dan kwallon Najeriyan daya fi kowane yawan kwallaye a gasar cin kofi Duniya

Home › › Najeriya taci Iceland 2-0: Ahmad Musa ya kafa tarihin zama dan kwallon Najeriyan daya fi kowane yawan kwallaye a gasar cin kofi Duniya

Kwallo biyun da Ahmed Musa ya zura a minti na 49 da 75 sun bai wa Najeriya damar da doke Iceland da ci 2-0 a gasar kofin duniya.


Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar hada maki uku bayan wasa biyu.

Kuma a yanzu ita ce ta biyu a rukunin bayan Croatia wacce tuni ta kai mataki na gaba bayan da ta doke Argentina da ci 3-0 a ranar Alhamis.

A yanzu Ahmed Musa shi ne dan kwallon da ya fi kowanne ci wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ya zura hudu.

Najeriya za ta kara da Argentina a wasan ta karshe na rukunin D domin fayyace kasar da za ta bi Croatia domin zuwa zagayen kifa-daya-kwala 'yan 16.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: