Friday, 22 June 2018
Jan hankali ga samari masu yiwa 'yan mata tambayar kwa-kwa

Home › › Jan hankali ga samari masu yiwa 'yan mata tambayar kwa-kwa
Sanannen me fadakarwarnan a shafin sada zumunta na Twitter da ake kira da Mustafa ya ja hankalin samari masu yiwa 'yan mata tambayar kwa-kwa tun kamin su auresu, ya fara da cewa:

(Sai kaji saurayi nawa budurwa tambayar)
Ina zaki?

Dawa kike waya?

Waye a DP dinki?

Ya naga kina Chating kina dariya?

Me yasa kike numfashi?.

Yace, haba dan uwa,
Kai ba gaisuwa ba.
Kai ba sadaki ba.
Kai ba aure ba.
Sai binciken tsiya.
Toh ka aureta mana kawai ka huta da wannan zargin haka, kar ka sawa kanka hawan jini fa. Toh.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: