Thursday, 14 June 2018
Ali Nuhu ya karyata cewa ya fito takarar gwamnan jihar Kano

Home Ali Nuhu ya karyata cewa ya fito takarar gwamnan jihar Kano

Irin wadannan hotunan dake nuna cewa tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya fito takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam'iyyar APC sun rika yawo a shafukan sada zumunta da muhawara amma Alin ya fito ya karyata hakan.

Ali Nuhu ya fito ta kafafenshi na sada zumunta da muhawara inda yayi kira ga jama'a da su yi watsi da wancan labari ba gaskiya bane.

Ga abinda ya rubuta kamar haka:

'Ire-iren wadannan hotunan da suke yawo a shafukan sada zumunta ba gaskiya bane/Kindly disregard such posts #fakenews Kannywood,

Ko da a wata hira da yayi da bbchausa kwanannan Ali Nuhu yace bashi da ra'ayin fitowa takarar siyasa, harkar fim ce kawai a gabanshi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: