Saturday, 9 June 2018
Alhamdulillahi, naga(daren) Lailatul Qadri - Inji Adam A. Zango

Home Alhamdulillahi, naga(daren) Lailatul Qadri - Inji Adam A. Zango

Gadukkan alamu wani gagarumin abin farin ciki ya samu tauraron fina-finan Hausa kuma Mawaki, Adam A. Zango, duk dadai adamun be fito fili ya bayyana ainihin abin farin cikin da ya sameshi ba amma alamu na nuna cewa kamar ya zama jakadan kamfanin lemun Coca-cola ne.

Adamun yayi amfani da kalmomin' Alhamdulillahi, Naga Lailatul Qadri, Allah nagode da irin Alkhairin da nasarar da kake bani' wajan nuna farin cikinshi.

Lamarin ya dauki hankulan mutane da dama inda aka ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi.

Koma dai menene muna taya Adam A. Zango murna, da fatan Allah ya kara daukaka.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: