Sunday, 13 May 2018
'Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Home 'Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan tare da tauraruwar fim din Hausa da tauraruwar ta ta lafa, Zainab Indomie, Adamu ya bayyana cewa yana tare da ita cikin daukaka da rashinta, cikin arziki da talauci, ya kare da cewa Allah yi miki Albarka Indo.


A bayadai tauraruwar Zainab ta haskaka sosai a fina-finan Hausa amma sai aka dena jin duriyarta, an yita surutai iri-iri akan abinda ya sa aka daina jin duriyar Zainab ciki hadda wanda aka rika cewa ciwon kanjamaune ya kamata.

Amma ta fito ta karyata hakan harma tayi Allah ya isa ga duk wanda suka mata wancan kazafin.

A 'yan kwanakinnan dai Zainab ta fito ta bayyanawa Duniya cewa ta dawo harkar fim.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: