Wednesday, 16 May 2018
Me yasa fina-finan Hausa suka fi raja'a akan labaran soyayya?

Home Me yasa fina-finan Hausa suka fi raja'a akan labaran soyayya?

Wata baiwar Allah tayi kira ga masu shirya fina-finai na masana'antar fim din Hausa da cewa bafa soyayya da rayuwar aurece kadai a yankin arewacin Najeriya ba, akwai abubuwa da dama da za'a iya yin fim a kansu, ta bayyana damuwa akan yanda fina-finan Hausa suka ta'allaka a kan labaran sosayya kawai, inda ta kare zancen ta da cewa, Haba kowane fim soyayya.

Wannan kira nata da tayi a dandalinta na shafin sada zumunta na Twitter ya dauki hankulan mutane da dama inda aka bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

Wani dai cewa ayayi, babban abu shine irin yanda wasu ke tunanin fim matattarace ta bata tarbiyyar jama'a kuma masu yinshi mutanene da basu da tarbiyya, sai an canja irin wannan tunani, mutane sun san rawar da fim yake takawa a tsakanin al-umma sannan za'a iya samun canji.

Wasu kuwa cewa sukayi ba laifin masu shirya fina-finan bane, sun lura da irin abinda mutane suka fi so ne shiyasa suke basu shi.

Wasu kuwa sun goyi bayan wannan baiwar Allahn ne inda suka bayyana cewa gaskiya yawan fina-finan soyayya da ake samu a fina-finan Hausa abin yayi yawa, ya kamata a samu canji.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: