Monday, 7 May 2018
'Duk me kurin shi dan asaline ko kuma yana hulda ta turawa ya nuna mana UBANSA Inji - Sanata Shehu Sani

Home 'Duk me kurin shi dan asaline ko kuma yana hulda ta turawa ya nuna mana UBANSA Inji - Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya saka wani tsohon hoton mahaifinshi, Alhaji Muhammad Sani Hassan inda yake tare da turawa a jihar Kaduna, Sanatan ya rubuta cewa duk me kurin hudda da turawa ko kuma shi dan asaline to ya saka hoton ubansa.

Gadai abinda sanatan ya rubuta kamar haka:

'My Late father Alhaji Muhammad Sani Hassan in 1972 in Kaduna.Duk dan ‘Asali’, ko mai kurin hudda da turawa ayau yayi posting HOTON UBANSA.'

A makon daya gabatane dai akaji gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai na tsinewa sanatocin jihar ciki hadda Shehu Sani saboda kin amincewa gwamnatin jihar ciwo bashi, a cikin bidiyon gwamnan ya kira sanatocin da wadanda basu da asali.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: