Sunday, 27 May 2018
Mawakin Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har Naira Milyan Dari

Home Mawakin Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har Naira Milyan Dari

Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har
Naira Milyan Dari
JARIDAR DIMOKURADIYYA
Anyi cirko-cirko a Ofishin kungiyar mawaka tun bayan
bullar rahoton mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi kwana
da makuden kudade sama da nera milyan Dari.

Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna
Aliyu Ningi dake jihar Bauchi shiya bayyanawa manema
labaru, yace Gwamnan Jihar Zamfara shiya basu kudin
bayan sun bukacin hakan kan irin gudun mawar da suka
bayar a gabanin zabukan 2015 gashi kuma sun shirya
bayar da gagarumar gudun mawa a zabukan 2019 dake

tafeTunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo
kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar
Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin
sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden
ya basu nera milyan goma sha takwas inji Haruna Ningi.

Ya kara da cewar a matsayina na shugaban kungiya har
zuwa yau Dauda bai taba yi mun maganar ba, bayan
lokacin dana sake tun tuba sa sai yace har yanzu ba’a
cika ragowar kudaden ba amma na kusa dashi wanda
shima yana daga cikin mawakan mai suna Oris yace tuni
an baiwa Rarara ragowar nera milyan Arba’in din.

To a hakan dai muka bukaci nera milyan Arba’in da biyu
da suka rage a hannun shi ya kawo su azo a zauna a
tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar shi na banki
ya sami matsala.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: