Thursday, 10 May 2018
Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Home Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kenan a wadannan hotunan da take tare da wanda ake sa ran shine zata aura, Maryam ta saka hotunan dake nuna alamar soyayya tsakanin ta da mutumin a dandalinta na sada zumunta.

Haka kuma wani abu dake kara nuna alamar akwai soyayya tsakanin Maryam da mutumin wanda ga dukkan alamu kamar magana har tayi karfi, shine irin kalaman da ta rubuta a tattare da hotunan.

Da farko dai Marya ta rubuta cewa, Ina tare da komai nawa.

Sanna kuma ta sake rubuta cewa, komai da lokaci idan kayi hakuri.Saidai maryam bata fito karara ta bayyana matsayin mutumin a gurinta ba, amma koma dai menene, lokaci be bar komai ba. Muna musu fatan Alheri.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: