Thursday, 10 May 2018
Mansura Isa tayi kira ga 'yan kasuwa kada su tayar da farashin kayan abinci saboda zuwan Azumi

Home Mansura Isa tayi kira ga 'yan kasuwa kada su tayar da farashin kayan abinci saboda zuwan Azumi

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansura Isa tayi kira ga 'yan kasuwa da su tausayawa talaka kada su tayar da farashin kayan abinci lura da irin yanda ya kusan zama al'ada duk lokacin da azumi ke gabatowa sai kaga kayan abinci sunyi tashin gwauron zabi.

Mansurah Isah tayi kira ga kamfanoni irin su Dangote da BUA da sauransu da su yi kira ga abokan huldarsu da suke sayarwa da kaya kada su tayar da farashin kayan abinci saboda al-umma su samu suyi azumi cikin wadata.

Da fatan Allah yasa sunji kuma su aikata, Allah ya saka mata da Alheri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: