Saturday, 19 May 2018
Karanta amsar da aka baiwa wani da ya tambayi cewa wai me Hausawa ke wa Najeriya da zata yi Alfahari dasu?

Home Karanta amsar da aka baiwa wani da ya tambayi cewa wai me Hausawa ke wa Najeriya da zata yi Alfahari dasu?

Wani mutum yayi wani rubutu a dandalinshi na sada zumunta da muhawara daya dauki hankulan mutane, abinda ya rubuta kuwa shine, Inyamurai na sa Najeriya Alfahari da 'yan kwallonsu, Yarbawa na sa Najeriya Alfahari da mawakansu, wai ta wace hanya Hausawa ke sa Najeriya Alfaharine?.

Ya sha amsoshi kala-kala amma wadda tafi daukar hankali itace wadda wani bawan Allah me suna Captain Mashi ya bashi.

Yace mai, Mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afrika kuma yafi kowane bakar fata kudi a Duniya dan Kano ne dake Arewacin Najeriya. Dangote yana saka kai, babanka, mamanka da dukkan danginka Alfahari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: