Sunday, 20 May 2018
Kalli yanda Mansurah Isah ta taimakawa wannan yarinyar

Home Kalli yanda Mansurah Isah ta taimakawa wannan yarinyar

Wannan wata yarinyace me suna A'isha da tayi fama da wani irin ciwo da ya fito mata a hannu, hannun nata ya kimbura, iyayen yarinyar basu da halin da zasu biya a mata aiki, wasu lokutan ma idan sunje asibiti ba'a kulasu, bayan da tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Matar Sani Danja, Mansurah Isah taji labarin wannan yarinyar, ta nema mata taimako kuma gashi har an mata aiki.

An kawo yarinyar daga garin Patiskum na jihar Yobe zuwa Kano inda anan ne aka mata aikin hannun, Mansurah ta saka wadannan hotunan inda suka nuna yanda take kula da A'isha bayan da aka mata aiki take kwance a gadon Asibiti.


Muna fatan Allah ya sakawa Mansurah da Alheri da tayi sanadin wannan abu da dukkan wadanda suka bayar da taimako dan inganta rayuwar wannan yarinya.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: