Monday, 21 May 2018
Kalli hotunan 'Mala'ika da aka dauka a kasar Amurka'

Home Kalli hotunan 'Mala'ika da aka dauka a kasar Amurka'
Kalli hotunan 'Mala'ika da aka dauka a kasar Amurka'

Wannan wasu hotunan da wani mutum me suna Thorman ya dauka ne dake Michigan a kasar Amurka, kyamarar dake gidanshice ta dauki hotunan da dare inda za'a iya ganin wata halitta me fiffike a saman motarshi, Thormas dai yace wannan hoton mala'ikane.

Ya dauki hotunan ya kai cocinshi inda limamin cocin nashi ya tabbatar da cewa Eh! Lallai wannan mala'ikane dake karesu da dare idan suna barci.

Cocin ta saka hotunan a shafukan sada zumunta, kuma sun dauki hankulan mutane sosai inda wasu suka yarda cewa Mala'ikane a wannan hoton wasu kuwa cewa sukayi wani kwarone kawai.

The mercury news.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: