Tuesday, 8 May 2018
Ina alfahari da Davido akan abinda yayi wa budurwarshi - Inji Mansurah Isah

Home Ina alfahari da Davido akan abinda yayi wa budurwarshi - Inji Mansurah Isah

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansura Isah ya tabayyana cewa tana alfahari da mawakin kudancin kasarnan, Davido akan kyautar da ya yiwa budurwarshi Chioma, Shi dai Davido ya yiwa budurwar tashi kyautar motar miliyoyin naira ranar da tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta, abinda ya dauki hankulan mutane sosai haka kuma yanzu budurwar tashi ta saka hannu akan wani kwantiraki na yin aiki da wani gidan talabijin.

Mansurah ta kara da cewa ba duka mazane ke iya yiwa matansu haka ba ballantama ace budurwa, tace, wasu mazan na hana matansu cigaba dan su samu damar juyasu yanda suke so.

A karshe mansurah tace idan dai Davido zai yiwa budurwarshi irin wannan sha tara ta arziki to lallai matarshi zata zama sarauniya kenan.
Share this


Author: verified_user

0 Comments: