Tuesday, 29 May 2018
Hankalin Rahama Sadau be kwanciya sai taci Tuwo miyar Kuka

Home Hankalin Rahama Sadau be kwanciya sai taci Tuwo miyar Kuka

A wata hira da yayi da jaridar Daily Trust, dan uwan tauraruwar fina-fina Hausa da turanci, Rahama Sadau watau Haruna, ya bayyana irin yanda Rahamar take matukar son tuwon shinkafa miyar kuka.

Haruna yace duk ranar da akace tuwon shinkafa miyar kuka za'ayi a gida to ranar Rahama bata da hutu,haka zatayi ta zarya a dakin dafa abinci dan ganin anyishi yanda ya kamata kuma ba zata samu nutsuwa ba har sai an kammala taci.

Haka kuma idan akan hanya take taji ance yau tuwon shinkafa za'ayi to ta fara murna kenan.

YA TONA MIN ASIRI:

bayan data ga wannan labari, Rahama ta bayyana cewa ' Malam Haruna duk yabi ya tona min asiri.


Ali Nuhu ma da ya ga labarin ya tsokane ta inda ya kirata da Acici.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: