Wednesday, 30 May 2018
Bace min da gani - Inji Rahama Sadau ta fadawa wani daya bata shawara

Home Bace min da gani - Inji Rahama Sadau ta fadawa wani daya bata shawara

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta taya wani abokin aikinta da sukayi shirin fim din turanci tare murnar zagayowar ranar haihuwarshi, inda ta kirashi da mijinta a dandalinta na sada zumunta, wannan batu ya dauki hankulan mutane inda wasu suka rika tambayar tayi aurene?.

Wani ya jawo hankalin Rahamar inda yace ta rika fadin abu a zahiri yanda yake mana, kamata yayi tace mijinta a fim ba a gaske ba.

Ya kara da cewa yanzu idan wata kafar watsa labarai tace wani abu akan wannan batu sai ki zo kina fadin Allah ya isa bayan kuma kece kika bada kofar hakan.

Rahama dai ta bashi amsar cewa ya fice mata daga shafinta.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: