Thursday, 3 May 2018
An yi jana'izar fitacciyar jarumar Kannywood Hauwa Maina

Home An yi jana'izar fitacciyar jarumar Kannywood Hauwa Maina

An yi jana'izar fitacciyar jarumar Kannywood Hauwa Maina a Kaduna da safiyar Alhamis.

Jarumar ta rasu ne a ranar Laraba da daddare. Wani makusancinta ya shaidawa BBC cewa ta rasu ne a Kano bayan ta sha fama da jinya.

Hauwa Maina na daga cikin matan da suka jima suna fitowa a fina-finan Hausa.
Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama.

Fim din ta na farko shi ne Tuba wanda Malam Yahya wani tsohon ma'aikacin gidan talabijin na kasa NTA ya bayar da umarni.

Ta fara fitowa a matsayin budurwa, sai kuma matar aure, sannan ta koma tana fitowa a matsayin uwa.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa da ba a kai ga wallafawa ba, Hauwa Maina ta ce ba kowane irin fim take amincewa ta fito ba.

Ta ce tana fitowa ne kawai a fim din da ta gamsu cewa labarinsa ya yi ma'ana, kuma zai ilmantar.

Tuni dai jarumai na fina-finan Hausa suke ta bayyana alhini dangane da rasuwar jarumar, wacce da dama ke dauka a matsayin uwa.

Bayan fina-finan Kannywood, Hauwa Maina ta kuma fito a fina-finan Nollywood na kudancin Najeriya da ake yi da turanci.
Ita ce ta fito a fina-finai na tarihi kamar Quen Ameena sarauniyar Zazzau, da sarauniya Daurama.

Ta'aziyya

Jaruman fina-finan Hausa na Kannywood suna ci gaba da nuna jimami da alhinin rashin marigayiyar.

A sakonnin da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta na Instagram, jaruman sun yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayiyar.

bbchausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: