Saturday, 19 May 2018
Akwai gyara a halayen 'yan Najeriya inaga sai anyi juye kaminn a samu canji - Inji Tantiri

Home Akwai gyara a halayen 'yan Najeriya inaga sai anyi juye kaminn a samu canji - Inji Tantiri

A sakon da ya fitar na taya masoyanshi murnar ranar Juma'a, tauraron fina-finan Hausa kuma me bayar da umarni, Abdulmimin Iliyasu Tantiri ya bayar da labarin yanda ta kaya tsakaninshi da wani me sayar da dankalin turawa da yace me zagin shugaba Buharine, ya bashi kudin dankali tun tuni amma da aka kwana biyu yaje amsa, kuma bawai ya sayo wani sabon dankalin bane, sai yace mai ai ya tashi.

A cikin jawabinshi, yace anya kuwa ba sai anyi juyen Mutanen Najeriya ba kamin a samu canji?.

Ga bayanin nashi kamar haka:

'Akwai damuwa matuka akan halayen wasu yan Nigeria musulmai,wani mutum mai yawan zagin Baba Buhari a area mu yana sayar da dankali turawa da kuma kwai yau yakai sati daya na bashi kudi akan 850 kwando na dankali #950 kuma na kwai jiya naje karba sai yake gaya mun kayan nan sun tashi Dankali ya koma #1300 kwai kuma #1100 duk da cewa bawai sabon kaya ya siyo ba kuma naga wadanda suke shagon wasu buhunhuna da na gani lokacin cinikin da mukayi ba a taba su ba ma.

Da irin wannan rayuwa ta Ina shima talaka zaiga daidai?Kowa dama yake jira idan tazo kawai zai yi iya yinsa don ya azurta kanshi.

Nigeria dai sai Allah inaga sai dai idan juye za'ayi wa kasarnan sannan za'a samu dama.Allah ka iya mana .

JUMMAT/RAMADAN MUBARAK'

Share this


Author: verified_user

0 Comments: