Sunday, 20 May 2018
Adam A. Zango zai yi waka da Davido ne?

Home Adam A. Zango zai yi waka da Davido ne?

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya saka wannan hoton na tauraron mawakin Najeriya, Davido sannan yayi wata magana dake nuna alamar kamar zasu yi aiki tare.

Adamu yace, Obo na nagode, wani babban abu na hararata, Allah kaine mai lokaci kuma ka bani sannan kana kan ara min!! Allah Nagode.


Adamu dai bai fito ya bayyana hakan ba kai tsaye amma wannan magana tashi tana alamta haka, idandai hakan ta faru Adamu zai zama zakaran gwajin dafi tsakanin mawakan Arewa. Koma dai menene lokaci zai bayyana mana.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: