Thursday, 17 May 2018
Adam A. Zango ya nemi yafiyar jama'a

Home Adam A. Zango ya nemi yafiyar jama'a

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya fitar da wani sako ta dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya roki duk wani wanda yayi wata mua'a mala dashi da ya yafe mai 'dan akwai wanda ba zasu kai karshen Ramadanaba, wata kila ina cikinsu' kamar yanda ya bayyana.

Ga sakon Nashi kamar haka:

'Wannan shine rana ta farko na watan ramadan. Hakika na san akwai jama'ar Musulmai da dama Wadanda bazasuga karshen wannan RAMADHAN dinba....

Allah shine masanin fili da boye, Watakil ina cikinsu.


Don haka nake neman afuwa awajen dukkan wanda yake da wani hakkinsa akaina, da kuma duk wanda muka taba yin wata Mu'amala da su.

Ni dai na yafewa kowa, kuma ina neman afuwa awajen kowa da kowa. Allah Ubangijinmu mai afuwa ne, mai rangwame ne. Kuma yana son masu rangwame daga cikin bayinsa.

NAGODE........'

Share this


Author: verified_user

0 Comments: