Monday, 16 April 2018
Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje yasa ba'ajina a fim: Masoyana ku tayani da addu'a ina matukar son yin aure:Yanda Abdu Boda ya yaudareni: Ban taba lalata ba - Inji Fati Bararoji

Home Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje yasa ba'ajina a fim: Masoyana ku tayani da addu'a ina matukar son yin aure:Yanda Abdu Boda ya yaudareni: Ban taba lalata ba - Inji Fati Bararoji

Jaridar Blueprint tayi hira da tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Baffa, Bararoji wadda tayi bayani akan rayuwarta da kuma dalilin da ya sa har yanzu bata yi aure ba, haka kuma Fati ta bayyana irin yanda suka yi soyayya da tauraron mawakin Hausa, Abdu Boda da kuma yanda ya yaudareta.

An fara da tambayar Fati dalilin da yasa ba'ajin duriyarta a masana'antar fina-finan Hausa inda ta kada baki tace, yawan tafiye tafiye da takeyi zuwa Dubai, Saudiyya da Indiya yin kasuwancin kayan adon mata yasa bata samun lokaci.

Ta kara da cewa tun bayan da ta shirya fina finai biyu masu suna Bakar Tukunya da kuma Jan Ido, sai ta lura cewa masana'antar tasu ta canja ba kamar yanda ta santa ba, shi yasa ta kama kanta ta koma gefe ta riki kasuwanci.

Da aka tambayeta dangane da rayuwarta a halin yanzu Fati ta fara da cewa, inaso inyi amfani da wannan dama dan yin kira ga masoyana da su taya ni da addu'a saboda na kosa inyi aure nima in haihu.

Ta kara da cewa a matsayina na mace musulma kuma na wuce shekaru talatin ina samun matsin lamba daga gurin iyayena akan yin aure, amma maganar gaskiya itace kyawawan maza da masu kudi na ta kawo min hari amma matsalar itace idan suka zo sai suce mu fita yawo kuma su bukaci in bisu otal ko kuma gidan hutawarsu, to gaskiya kuma kasan idan mace da namiji suka kebe na ukunsu shedanne shiyasa ban yarda da irin waccan rayuwar.

Ta kara da cewa shi yasa koda kazo inda nake sana'ar sayar da abinci da wuya ka ganni saboda wasu suna zuwane dan su sami damar gayyata ta wajan irin waccan harkar, matsalar maza itace suna tunanin kowace mace haka take, ko kuma da 'yan kudi kadan zaka rude ta tayi lalata dakai amma ba haka batun yake ba.

Da aka tambayi Fati akan batun maganar auren wani tauraro a cikin masana'antarsu da akace zatayi, tace, labarine me tsawo da ban takaici amma duk da haka zata dan gutsirawa mutane kadan suji.

Fati tace ba wani bane da ake cewa zata aura, tauraron mawakin jihar Katsinane Abdu Boda, sunsha soyayya, ya zama kamar dan gidansu, zai shiga gidansu kanshi tsaye, koda bata nan kanwarta zata dafa mishi abinci yaci.

Kwatsam sai taji labarin za'a daura mishi aure, wata kawarta ta kirata tace taga katin gayyatar aurenshi amma ba sunanta bane a jiki, tana jin haka taji kamar ta suma, ta dauko waya ta kirashi, ashe ranar data kirashidin ranar ne ake daura mishi auren, amma yace mata ba gaskiya bane.

Ta kara da cewa ta shirya ta dauki mota ta tafi katsina, aka sha hidimar biki da ita kuma ta nuna kamar babu abinda ke damuta, ana kammala bikin ta tafi Umara inda ta roki Allah ya taimaketa akan wannan batu ya kuma saka mata mafita, ta kara da cewa har gobe bata daina son Boda ba kuma bata rikeshi a rai ba dangane da binda ya mata.

Fati ta kara da cewa bata jin dadin irin yanda take cikin sa'anninta wanda yawanci duk sunyi aure, idan ta shiga masana'antar fim din Hausa takan ga sabbin fuskoki wanda wasunsu ma da tayi aure ta isa ace ta haifesu amma babu yanda zatayi hakanan take hakuri tana hulda da musamman wanda sukayi zamani tare irin su Sa'adiya Gyale da Rukayya Dawayya, tana jin dadi idan tana tare dasu.

Da aka tambayi Fati maganar yanda wasu sa'anninta a masana'antar fim suka tsere mata ta bangaren Arziki, cewa tayi, akwai wani labari na wata yarinya 'yar makaranta da akawa ciki amma da aka tambayeta wa ya mata ciki ta hakikance cewa ita bata taba lalata da kowa ba.

Haka kuma akwai labarin dan siyasa dake hira da wata macen banza akan cewa ta yarda dashi shi mutum ne me gaskiya itama ta gayamai cewa duk da yawon lalatar da tayi itama fil take a leda bata rasa budurcin taba.

Fati tace ta kawo wadancan misalaine dan gugar zana, kuma Allah yasa an fahimta, ta kara da cewa da ta yarda tayi rayuwa irin ta sharholiya da motoci da gwalagwalai babu irin wanda ba zata samu ba amma ta zabi ta rike mutuncinta bata taba saka kanta cikin irin waccan harka ba, shi yasa ma take harkar sayar da abinci da kuma tafiye-tafiye zuwa Dubai da Saudiyya da Indiya dan samun kudinta ta tsarkakakkiyar hanya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: