Wednesday, 25 April 2018
Kaji Sana’ar Da Ni Ke Yi Bayan Na Daina Fitowa Fina-Finan Hausa – Inji Sadiya Gyale

Home Kaji Sana’ar Da Ni Ke Yi Bayan Na Daina Fitowa Fina-Finan Hausa – Inji Sadiya Gyale

Sadiya Gyale, wannan suna ne da ya jima yana yin tashe a cibiyar shirya Fima-fimai wacce aka fi da kira da, ‘Kannywood.’ Kamar sauran tamkar ta, Sadiya Gyale, ta daina fitowa a cikin shirye-shiryen Fima-fiman, bayan ta kwashe shekaru masu yawa da za a iya cewa kusan tun farkon kafuwar cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood.


Ta yi zamanin da fuskanta mafiya yawan mutane ke son gani a cikin Fim din, masu shirya Fima-fiman da masu bayar da umurni duk ribibinta suke yi.

Kamar yadda masu sha’awan kallon Fima-fiman ke shaukin jin sunanta da kuma ganin fuskanta a cikin Fima-fiman.

To wace ce Sadiya Gyale, tana ina ne kuma a halin yanzun, bayan barin ta cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood, me take yi ne a halin yanzun, wace shawara kuma take da ita ga ‘yan fim din na yanzun, musamman mata?

Duk amsoshin wadannan tambayoyin da ma wasun su suna cikin abin da za ku karanta a wannan hirar na ta.

A sha karatu lafiya: Muna so ki fada mana cikakken tarihin rayuwar ki?

Assalamu alaikum, kamar yanda ku ka sani, Suna na Sadiya Muhammad (gyale), an haife ni a Lagas ne, a watan Satumba shekarar 1985, iyayena duka Fulani ne, na yi karatun Firamare da Sakandare a Kano, na gama Sakandare a T/wadan Dankadai, na shigo’Industry,’ a shekarar 2003.

Alhamdulillah, mun yi lafiya mun gama lafiya, muna yi wa sauran fatan alheri.

Bayan kin bar fitowa a Fima-fimai, akwai wani aikin ko sana’an da ki ka koma yi ne, ko kuma makaranta ki ka koma?

Bayan na daina fitowa a Fima-fimai, ina sana’o’i kala-kala, na saye da sayarwa, da noma duk ina yi.

Mun ga kin samu shaidar yabo, ko za ki yi mana bayani kan yadda aka yi ki ka samu?

Wata kungiya ce ta makaranta Mujaallar fim, su ne suka karrama ni, da ma sun taba karrama ni, ban samu damar halarta ba.

Malama Sadiya, ya ya batun aure, yaushe za ki kara kiran mu mu rakashe?

Insha Allah muna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.

Ko Kina da sha’awan zama mai bayar da umurni ko mai daukan nauyin shirya Fima-fiman ne, na kanki bayan kin yi aure?

Daman can nakan dauki nauyin shirya Fima-fiman, kuma ko na yi aure ma zan ci gaba da hakan.

Ta ya ya aka yi ki ka samo lakabin sunan “Gyale”?

Na samo sunan gyale ne a fim din gyale, fim din gyale shi ne fim di na na farko, wanda na fara yi, wannan ne ya sa ake kira na da Sadiya gyale.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: