Friday, 27 April 2018
Hukuncin Ma’auratan Da Suka Nisanci Junansu – Daga Zauren Fiqhu

Home Hukuncin Ma’auratan Da Suka Nisanci Junansu – Daga Zauren Fiqhu

HUKUNCIN MA’AURATAN DA SUKA NISANCI JUNANSU :
TAMBAYA

********************

Assalamu Alaykum mallam ya aiki?

Don Allah mallam ina da tambaya
Me hukkuncin mata da miji da suka nisanci kansu na tsawon wata 6 (six months).

Bissalam
AMSA
*******

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ma’auratan da suka nisanci junansu har tsawon watanni shida, Hukuncinsu yana rataye da dalilin da ya janyo hakanne.

Misali :

1. Idan larura ce daga shi Mijin ko kuma Matar, to wannan babu komai mutukar dai yin hakan ba zai chutar da ‘daya bangaren ba.

2. Idan ita Matar ce ta kaurace ma shimfidar Mijinta ar tsawon wannan lokacin domin wani ra’ayi nata ko kuma don bijire ma Mijinta, to tabbas ta aikata laifi mai girma.

Domin kuwa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa :

“IDAN MUTUM YA KIRA MATARSA ZUWA SHIMFIDARSA AMMA BATA JE MASA BA, SAI YA KWANA YANA FUSHI DA ITA, TO MALA’IKU MA SUNA TSINE MATA HAR SAI TA WAYI GARI”.

To wannan hukuncin wacce ta aikata hakan a dare daya kenan. To yaya kuma wacce har tayi watanni shida acikin haka?.

Idan kuma shi Mijin ne ya kaurace ma matarsa har tsawon wadannan Watannin ba tare da wata larura ko halastaccen dalili ba, sai don son rai, to hukuncinsa shine za’a tsayar dashi a tambayeshi shin menene manufarsa cikin abinda yakeyi din nan?. Shin ya saketa ne ko kuma tana nan amatsayin matarsa?.

Idan yace eh ya saketa shikenan sai taje tayi iddah ta auri wani Mijin. Idan kuma yace tana nan amatsayin matarsa to sai a Umurceshi cewa yaci gaba da Mu’amalar aure da ita. Idan yaci gaba da yi shikenan. Idan kuma yaqi kusantarta sai a bashi tsawon watanni hudu (ya zama hukuncin Eela’i kenan). Idan bai sadu da ita ba, sai a raba auren.

WALLAHU A’ALAM.

Ya kamata ma’aurata su rika yi ma Junansu afwa kuma su rika kokarin warware matsalolin zamantakewarsu atsakaninsu ba tare da sai wasu sun shigo musu ba. Kamar yadda Mace zata iya samun mummunan sakamako awajen Allah idan batayi ma mijinta biyayya ba, to shima Mijin nata idan ya zamanto azzalumi mai danne hakkokin iyalinsa to lallai shima zai tarar da sakamakon zaluncinsa a lahira.

DAGA ZAUREN FIQHU.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: