Saturday, 14 April 2018
Hausa Hip-Hop: Wanene Cassik ?

Home Hausa Hip-Hop: Wanene Cassik ?

Buba Barnabas, wanda a ka fi sa ni da Classiq, mawaki mai cika da salo da kyale-kyale a wakokinsa na Hausa Hiphop.

Classik dan asalin garin Bauchi, ya kuma taso ne a Kano, inda ya yi karatunsa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya karanci Computer Science, daga bisa ni kuma ya koma Jos, don cigaba da harkokinsa na waka.

Ya yi aiki ne tare da Kungiyar “Finese Entertainment” Har na tsawon shekara biyar a bisa yarjejeniyar kwantiragi.

A cikin shekarar 2018 ne kwantiraginsa ta kare, inda ya kirkiri kungiyarsa mai taken Arewa Mafiya. Sunansa na gayu ya yi daidai da salonshi na waka, don kuwa shi ya kan yi wakokinsa ne da salo daban-daban.

Za a iya ciwa a mawakan Nijeriya bakidaya zai yi wuya a samu mawaki mai salonsa.

Classik shi ne matashi na farko da ya fara waka da kananan shekaru a wancan lokacin, don rahotanni sun nuna ya fara waka tun ya na dan shekara 16, ya samu karbuwa kwarai a Legas.

Kwanan nan ya fitar da wani sabon bidiyon sa mai taken “Gudu”, inda ya saka daya daga cikin shahararrun mawakan kasar nan kuma haifaffen garin Jos MI Abaga.

Shekarun baya ya yi bidiyon waka da fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, mai taken “I Lobe U”.
Haka nan daya daga cikin wakokinsa da su ka yi suna ita ce “Duniya”.

©Leadership

Share this


Author: verified_user

0 Comments: