Friday, 20 April 2018
'Babu cin hanci a gwamnatin shugaba Buhari - Inji Osinbajo

Home 'Babu cin hanci a gwamnatin shugaba Buhari - Inji Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa irin matakan da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu buhari ta dauka yasa ba'a samu cin hanci karkashin gwamnatin tasu ba.

Ya bayyana hakane a lokacin da yake amsar bakuncin tawagar wasu 'yan kasuwa da suka kaimai ziyara ofishinshi a Abuja, Osinbajo ya bayyana cewa rashin rashawa da cin hanci a gwamnatin shugaba Buharin ya samar da kudade da dama da za'awa 'yan Najeriya ayyukan raya kasa dasu, ya kuma kara da cewa nan bada dadewa ba za'a fara ganin amfanin hakan.

Ya kara da cewa amma gwamnatin data gabata ta wawushe komai dake asusun gwamnati yanda takai har bashi saida suka ciwo, ya kara da cewa munin abinda suka iske ba'a taba samunshi ba a tarihin kasarnan.

Ya kuma ce abin takaici shine irin yanda gwamnatin bayan ta rika amfani da kudaden al-umma wajan rabawa mukarrabanta dan kawai su samu suci zabe.

Akan maganar amincewa da kasafin kudin wannan shekarar kuwa, Osinbajo ya bayyana cewa duk da yake kasafin kudin na gaban majalisa tun shekarar da ta gabata amma zasu yi kokarin ganin cewa majalisar ta amince dashi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: