Monday, 30 April 2018
Barcelona ta dauki kofin La Liga na bana

Home › › Barcelona ta dauki kofin La Liga na bana

Post By:


Barcelona ta ci kofin La Liga na 25 a kakar farko ta kociya Ernesto Valverde bayan da Lionel Messi ya taimaka ta doke Deportivo La Coruna 4-2.

Messi ya ci kwallo uku rigios a wasan da Barca ta yi fintinkau da ratar da ba za a kamo ta ba a teburin gasar da maki 86 a wasanta 34.

Barcelona ce ta fara shiga gaba a wasan da ci 2-0 sakamakon kwallayen da Philippe Coutinho da Messi suka zura.

Sai dai 'yan Depor sun tashi tsaye inda suka farke balabalan ta hannun Lucas Perez and Emre Colak.

A cikin minti goman karshe ne na wasan Messi ya zura biyu, wasan ya kasance 4-2.
Wannan shi ne kofin La Liga na 25 da

Barcelona ta dauka, bambancin takwas tsakaninta da abokiyar hamayyarta Real Madrid.

Wasa hudu ya rage a kammala gasar da har yanzu ba a doke Barcelonar ba.
bbchausa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: