Thursday, 12 April 2018
Bani da ƙawa a Masana'antar kannywood - Inji Jaruma Umma Shehu

Home Bani da ƙawa a Masana'antar kannywood - Inji Jaruma Umma Shehu
Shahararriyar jaruma wacce tauraronta ke kan haskawa a dandalin shirya fina-finan Hausa, Umma Shehu ta bayyana alakarta a farfajiyar Kannywood.

A cewar Umma bata da wata da ta rika a matsayin kawa a masana’antar saboda tana gujewa duk wani matsala ko abu da zai tunzura ta.

Jarumar ta jaddada cewa ita sana’arta kawai ta sanya a gaba saboda haka bata da lokacin kulla ko wace alaka ta kawance.

Idan dai bazaku manta ba a kwanakin baya ana ta ba’a ga jarumar bayan wani hira da tayi da Aminu Sheriff Momo a wani shirin talbijin sakamakon wani tambaya da ta kasa amsawa wanda ya shafi addini.

Jarumar ta kuma jaddada cewa ita batayi fushi ba akan abunda ya faru a tsakanin su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: