Sunday, 15 April 2018
Babban Dan Adam A Zango Ya zama mawakin Hip-Hop

Home Babban Dan Adam A Zango Ya zama mawakin Hip-Hop

Babban ɗan fitaccen jarumi Adam A. Zango, mai suna Ali Haidar Zango, ya fara waƙar hip pop.

Za a riƙa yi masa laƙabi da "Star Boy".

Ali, wanda aka fi sani da suna Haidar, da kan sa ne ya bayyana hakan a shafin sa na Instagram, inda ya sanar da mabiyan sa cewa waƙoƙin sa guda biyu su na nan fitowa da sunan 'Godiya' da kuma 'Rayuwa'.

Ya kuma tura da saƙo inda ya bayyana cewa mahaifin sa ne ya gano basirar da Allah ya ba shi.

Haidar ya sha alwashin ba zai ba mahaifin nasa kunya ba a wannan aiki da ke gaban sa.

Mujallar Fim ta gano cewa har an kammala shirye-shiryen ɗaukar bidiyon wani ɓangaren na waƙoƙin matashin mawaƙin.

Baban sa ya aika da wani guntun bidiyon waƙar Haidar ɗin a shafin sa na Instagram wadda ba ta wuce minti ɗaya ba.

A tattaunawar sa da mujallar Fim, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a kammala aikin bidiyon waƙoƙin guda biyu ba, amma da zarar an gama za a sake su baki ɗaya, na gani da kuma na saurare.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: