Sunday, 15 April 2018
Auren Jaruma Sadiya Kabala Yazo

Home Auren Jaruma Sadiya Kabala Yazo

A RANAR Asabar ɗin wannan makon, wato 14 ga Afrilu, 2018, za a ɗaura auren ɗaya daga cikin jarumai mata da ke Kaduna, wato Sadiya Kabala.

Za a ɗaura auren ta da sahibin ta mai suna a masallacin Juma'a na Al-Mannar da ke Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

A kwanaki Jaruma ta bayyana a kafar Sada Zumunci Cewa Tana Matukar son tayi aure Gashi Yanzu Allah ya kawo mata.

A jerin tsarin bikin wanda mujallar Fim ta gani, an nuna cewa za a fara shagalin auren a ranar Alhamis ɗin nan a lambun shaƙatawa na Ƙofar Gamji.

Bayan ɗaurin auren kuma za a yi dina a wani otal mai suna Silver Sand da ke Titin Katuru, Unguwar Sarkin Musulmi.

To Allah ya sa a ce gara da aka yi, amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: