Sunday, 4 March 2018
Sharhin fina finai : Sharhin Fim Din Saudat Sabon Shiri

Home Sharhin fina finai : Sharhin Fim Din Saudat Sabon Shiri
Suna: Saudat

Tsara labari: Shafi’u Dauda Giwa

Producer: Abba Abubakar Babaye

Bada umarni: Falalu A Dorayi

Kamfani: Babaye International Nig Ltd

Jarumai: Adam A Zango, Fati Washa, Rabi’u Rikadawa, Ladidi Tubless, Fati S.U, Abdullahi Abbas, Nura MC, da Umar But cut.

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna Nabil(Adam A Zango)suna shawara da yaransa acikin wani katafaren gida shawarar gidan da zasu fada fashi a ranar domin an nuna kasurgumayen ‘yan fashi da makami ne a lokacin suka yanke shawarar zuwa gidan wani babban mai kudi Alh.Mukhtar suka shirya a daren suka tafi suna zuwa suka tasa shi a gaba da matarsa Hajiya(Ladidi Tubless) suka ce sai ya fito musu da kudi domin sun sami labari ya shigo da milyan ashirin gidan, Alh.Mukhtar har fara gardama amma saboda ya ga da gaske dai kasheshi zasu yi ta sanya ya dakko musu wannan milyan ashirin ya damkamusu suka fita daga dakin sannan suka fada dakin wasu ‘yan mata su uku ‘ya’yan kanwar Hajiya ne suka zo gidan hutu nan ma suka tsorata su ba tare da sun yi musu komai ba suka fito suka shiga dakin ‘yar gidan Saudat(Fati Washa) Nabil ya sai ta ta da bindiga yana tsorata ta amma daya fuskanci babu tsoro a tattare da ita sai jikinsa ya fara mutuwa Saudat ta tsaya ta fara yi wa Nabil wa’azi akan abinda yake yi haramun ne domin Allah baya yafe hakkin wani akan wani ta kawo masa aya da hadisi ta kashe masa jiki a lokacin ya fara nadamar abinda yake yi na fashi da makami, bayan ya koma gida sai tunani da nazari suka shige shi kwata kwata sai ya yi alkawarin ya dai na sata ya umarci yaransa da su dawo da kudadan daya raba musu aci-kin wannan milyan ashirin din ta gidan Alh. Mukhtar, acikin yaransa wasu suka amince kai tsaye wasu kuma sai da suka bijire masa ba a son ransu ba kowanne yadawo dashi Nabil yadauka yaje gidan Alh.Mukhtar ya kirawo Saudat ya ba ta wannan kudi da suka yi fashinsa sannan daga ba-ya ya miko mata kokon barar soyyayarsa taki amince masa abisa sharadin cewar sai yaje ya gyara duk barnar da ya yi a baya tare da alkawarin cewar zai dawo mutumin kirki Nabil ya amince ya tafi yaje ya fara mayarwa da mutane dukiyarsu daya diba sai da ya gama kaf yadawo sannan ya fara tsabtatacciyar sana’a ta halak a lokacinda ya sake dawo wa Saudat yana sake miko kokon bararsa akan neman soyyayarta Saudat ta amince ita ma ta fara sonsa amma sai dai kash da ma-ganar tazo gida sai mahaifinta ya ki amincewa a bisa dalilin cewar ba zai baiwa ‘yarsa dan fashi ba hakan tasa ya kori Nabil
Nabil ya tafi cikin bacin rai kamar yanda itama Saudat take ciki saboda ta kamu da sonsa sosai itama, kuma kin amincewar bata saka Nabil ya koma tsohuwar sana’arsa ta fashi ba ya koma makarantar islama sannan yana cigaba da neman kudinsa sai daga baya da mahafin Saudat ya yi bincike ya sami labarin Nabil tuba na gaske ya yi sannan ya kirawo Nabil ya yi masa alkawarin zai ba shi auren Saudat.

Abubuwan birgewa:

1- Labari fim din ya sami tsari mai kyau
2- An nuna wa al’umma muhimmancin wa’azi da alkairan da jinsa da aiki dashi hakan yake hai-farwa.
3- An nuna illar abu mara kyau, sannan jaruman sun yi kokari gurin isar da sakon.
4-Labarin ya tafi kai tsaye bai karye ba har ya dire.

Kurakurai:

1- An sami matsalar daukewar sauti a wasu hotuna na fim din.
2- shin Nabil ba shida kowane yake rayuwa shi kadai? ko iyaye bashi da su? tunda aka fara fim din ba’a nuna su ba sannan ko’a baki ba’a fadesu ba.
2- An nuna Saudat yarinyace mai ilimin addini mai tsoron Allah amma Akwai gurinda aka nuna Saudat tana sallah mahaifiyarta tazo tana yi mata fadan ta fara harhada sallar ne? shin wanda yake da wannan halayyar ta yaya za’ayi ya dinga yin sallah ba akan lokaci ba ballantana har ya dinga harhada wata da wata.
3- A yanda aka nuna Alh.Mukhtar mai tarin dukiya baikamata ace a gidansa akwai dakin da za’a gani ba’a kawace ba ballanta har mutum uku a gansu suna barci akan katifa daya ba.
4- Lokacin da au Nabil suka shigo fashi gidan Alh.Mukhtar Akwai gurinda suke shigowa dakin ‘yanmata su uku suna barci sosai yanayin tashin da ‘yanmatan suka yi bai kamata ace wadanda suke wannan barcin bane domin sun nuna kamar dama sun san da shigowar su Nabil ne, ya ka-mata ace sun bari sun dan yi musu wani abu na tsoratarwa sannan su firgita su tashi.

5- A matsayin Saudat na yarinya mai tarbiyya a lokacin da Nabil ya kirawota a waya ya fadamata cewar ta fito yana waje har take cemasa sai ta sanar da iyayenta amma sai mai kallo yaga bata sanar din ba kuma ta fita wajen nasa.
6-Babu yanda za’ayi dan fashi yashigo gidanka ya yi maka sata kuma kaga yadawo maka da ita ba tare da ya boyemaka kansa ba kuma ka aminta dashi lokaci guda dole kayi tunanin wani abun ya kulla amma sai gashi kaf wanda Nabil ya mayarwa da kudi babu wanda yaji tsoro ballantana har ayi yunkurin hadashi da hukuma.
7- Ba’a nunawa mai kallo ba ta hanyar da Nabil yake sanin sirrikan Saudat ba da duk guraren da ya ke samunta.

8- A matsayin Saudat na yarinya mai tarbiyya baikamata ace tana soyyaya na tsahon lokaci da Nabil ba har suna haduwa har a wuraren cin abinci amma duk mahaifinta bai sani ba.
9- lokacin da mahaifin Saudat ya kori Nabil kuma ya yi alkawarin zai aurar da ita nan da sati daya shin wana dalilin ne ya hana ba’a aurar da ita din ba domin ba’a nunawa mai kallo ba sai gashi sai bayan shekara da faruwar hakan ya kuma kiran Nabil akan cewar ya turo iyayensa.

10- sutturar da aka nuna Nabil yana sakawa lokacin da ya talauce ba ta dace ba domin suttura ce mai tsada.
Karkarewa:
Fim din ya yi kyau kuma ya kayatar amma tun daga farko farkon fim din mai kallo ya san abinda zai faru a karshe saboda an sha yawaita yin ire-iren irin wannan fina-finan a finafananmu na hau-sa aga mutum yana mugun hali acikin al’umma amma dalilin mace ya shiryu. Wallahu a’alamu!!!

Share this


Author: verified_user

0 Comments: