Monday, 5 March 2018
Sanata Kwankwaso Ya Bada Tallafin Buhun Shinkafa Dubu 1, 200 Ga Iyalan Wadanda 'Yan Bindiga Suka Kashe A Kauyen Birane Dake Jihar Zamfara

Home Sanata Kwankwaso Ya Bada Tallafin Buhun Shinkafa Dubu 1, 200 Ga Iyalan Wadanda 'Yan Bindiga Suka Kashe A Kauyen Birane Dake Jihar Zamfara

...muna zaton wuta a makera, sai gata a masaka, cewar Sarkin Zurmi

Daga Mu'awiya Abubakar Zurmi

Bayan jajantawa tare da Allah wadai da kisan gillan da 'yan bindiga suka yi wa wasu bayin Allah a kauyen Birane dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cikin juyayi da bakin ciki ya bada tallafin shinkafa buhu dubu daya da dari biyu ga iyalan wadanda 'yan bindiga suka kashe, sannan ya yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin kawo karshen kashe-kashen al'umma a Zamfara da Nijeriya baki daya, ya kuma yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya a Zamfara da ma Nijeriya baki daya. Sannan ya yi add'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.

A lokacin da yake jawabi,Mai Mairtaba Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Muhmmad ya yi godiya ga Sanata Kwankwaso bisa namijin kokarin da ya yi na zuwa takanas ta Kano zuwa Zurmi domin ya jajantama al'ummar karamar hukumar mulki ta Zurmi da jihar Zamfara bisa wannan masifa da ta afku.

Mai Martaban ya ce suna zaton wuta a makera sai gata a masaka, daga karshe ya yi godiya ga Sanata Kwankwaso kuma ya yi addu'ar Allah ya maida shi gidansa lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: