Monday, 12 March 2018
Sakon Ali Nuhu Zuwa ga yayansa Fatima da Ahmad

Home Sakon Ali Nuhu Zuwa ga yayansa Fatima da Ahmad

Fitaccen jarumi kuma daya daga cikin masu hanu da shuni masana'antar shirya fim na Kannywood Ali Nuhu ya wallafa sabbin hotuna tare da yaran cikin sa Ahmad Nuhu da Fatima Nuhu.

Sarkin kannywood kamar yadda aka yi masa lakabi ya wallafa hotunan su tare a shafin sa na kafafen sada zumunta tare da rubuta sakon farin ciki bisa ni'imar da Allah yayi masa na samun ya'yan.

"Daya daga cikin kyata mafi soyuwa a gare ni da Allah ya bani shine samun diya ta" ya rubuta tare da hoton shi da diyar shi Fatima.

Ya kara da rubuta "Idan mutum ya zama uba to ya zamanto abun koyi ga dan shi". Auren shi da matar sa Maimuna Garba Ja Allah ya albarkace su da yara biyu Ahmad da Fatima.

Yaran dai suma sun bi sahun mahaifin su harkar wasan kwaikwayo. Ahmad da Fatima sun fito a fina-finai da dama kuma a cikin shekarar 2017 Ahmad Nuhu ya amshi kyuatar gwarzon shekara na bangaren yara yan wasan kwaikwayo a gasar city people awards.

Idan ba'a manta Ali Nuhu da dan shi Ahmad sun haska tare cikin wani shirin fim mai taken "Uba da da".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: