Tuesday, 20 February 2018
Zaman Aure Ya Fiye Mun Kudin Da Zan Samu Da Ma Komai Da Komai - Inji jaruma Hannatu Bashir

Home Zaman Aure Ya Fiye Mun Kudin Da Zan Samu Da Ma Komai Da Komai - Inji jaruma Hannatu Bashir
Jarumar tana daya daga cikin yan matan masana'antar Kannywood da zasu ajiye yin fim da zaran sunyi aure domin mayar da hankali wajen kula da iyali

Hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?.

Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.

Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya.

"Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma".

Hannatu wanda ta kwashi sama da shekara bakwai a dandalin nishadantarwa tayi karin haske game da zargin da ake yawan yi ma yan fim na cewa su yan iska ne.

A cewar ta mafi yawanci mata dake aikata hakan bata-gari ne wadanda suke fakewa da cewa su yan fim ne.

Tace mafi yawanci katin bogi suke yawo dashi da yin karya cewa su yan fim ne domin idan aka bibiya sau da dama  jaruman basu san da zaman su ba a masana'antar.

Tace irin hakan yana faruwa sosai kuma mafi yawanci ire-iren yan matan da zarar an kama su sai su fake da cewa suna fim tare da nuna katin shaida na karya.


Jarumar wanda ta shirya shirin Sarauniya, Kukan Kurciya da Mairo da dai wasu fina-finai daban tace yin fim sana'a ce kamar sauran sana'o'i kuma yadda ma'aikata ke zuwa masana'antar su haka suma ke zuwa daban farfajiyar su.

Akalla fina-finai hamsin ta fito a ciki cikin tsawon shekara bakwai da tayi a dandalin nishadantarwa ta kannywood.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: