Sunday, 4 February 2018
Wata Budurwa Ta Yi Takakkiya Daga Nijar Har Nijeriya Don Ta Ga Umar M. Shareef

Home Wata Budurwa Ta Yi Takakkiya Daga Nijar Har Nijeriya Don Ta Ga Umar M. Shareef

Wata Budurwa Ta Yi Takakkiya Daga Nijar Har Nijeriya Don Ta Ga Umar M. Shareef


Wata budurwa ta yi kafa-da-kafa tun daga jamhuriyyar Nijar har zuwa jihar Kadunar Nijeriya domin ganin kyakkyawan mawaki kuma jarumi, Umar M. Shareef

Soyayya gamuwar jini, inji masu hikimar zance, hakan ce ta faru a lokacin da wannan matashiya mai suna Maryam ‘yar shekara 17 ta yi tattaki tun daga kasar Nijar zuwa Najeriya kawai saboda ta hada ido da shahararren mawakin nan Umar M. Shareef.

Matashiyar ta fito ne daga yankin Maradi, inda ta bayyana cewa iyayenta basa tare da juna sannan kuma ita ta kasance mai yawan yawo hakan ya sa mahaifiyarta ke zarginta da aikata masha’a.

A cewarta wannan zargi ne ya fusata ta har ta yanke shawarar zuwa Kaduna don ta hadu da gwaninta Umar su yi waka tare, watakila hakan zai sa ta samu sukuni a zuciyarta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: