Tuesday, 6 February 2018
Wani ya zargi cewa General BMB bashi da Uba: Karanta abinda Bellon yace mishi

Home Wani ya zargi cewa General BMB bashi da Uba: Karanta abinda Bellon yace mishi

A shekaran jiyane mukaji abinda ba'a saba ji ba daga bakin tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello(General BMB), inda ya kutuntuma ashaliya, saidai daga baya, bayanda da yawa suka nuna basu ji dadin haka ba kuma suka gayamai hakan be kamace shi ba, ya fito ya bayar da hakuri, Bellon ya fito ya nuna cewa farin cikinshi ya dawo, to saidai wani ya zargeshi da cewa wai be da Uba.

Mutumin ya kara da cewa gara su me gidansu Luwadi ne yake yi amma shi, bellon su waye iyayenshi na Asali?

Bellon ya mayarwa da wannan mutim martani inda ya gayamai sunan mahaifiyarshi da na mahaifinshi da kuma sunayen 'yan uwanshi sannan yace ya je ya gayawa sarkin nasu cewa Allah ya haramta mace musilma ta auri wanda ba musulmi ba amma shi ya halatta.

Gadai yanda abin ya kasance.Da alama wannan abu ya fara yin kamari. Allah shi kyauta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: