Sunday, 11 February 2018
Tsohon Mijin Sadiya Gyale wanda ya saketa tun kafin ta tare a gidansa ya rasu

Home Tsohon Mijin Sadiya Gyale wanda ya saketa tun kafin ta tare a gidansa ya rasu

Daga IRO MAMMAN

Dukkan mai rai mamaci ne. Allah Ya yi wa tsohon mijin Sadiya Gyale, wato Alhaji Abubakar Muhammad, rasuwa.
Ya rasu a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya a ranar Litinin ɗin wannan makon.

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa Alh Abubakar, wanda babban ɗan kasuwa ne, ya rasu sakamakon ciwon hawan jini da ya kama shi, kuma ya rasu jim kaɗan bayan an kai shi asibiti.

Majiyar ta ce ya je Istanbul ne harkar kasuwancin sa kamar yadda ya saba, to sai Allah Ya yi ƙarshen tafiyar kenan.

A cewar majiyar, an tsara cewa za a kawo gawar sa Abuja daga Turkiyya ɗin washegari, wato Talata.

Shi dai marigayin, an ɗaura auren sa da fitacciyar jaruma Sadiya Gyale a kan sadaki N50,000 a ranar 10 ga Afrilu, 2015 a Kano.

Auren ya ja hankalin jama'a sosai, musamman masoyan jarumar, domin Sadiya na daga cikin matan fim da aka zaƙu a ga ranar auren su.

Hakan ya sa bikin auren ya samu halartar ɗimbin ƙawayen ta.
Amaryar da ƙawayen ta 'yan fim sun yi bikin auren har na tsawon kwana uku, daga ranar 21 zuwa 24 ga watan Mayu.

An yi dabdala a ranar farko a Gidan Ɗanhausa, da wani ɗakin taro da ke Bompai (inda aka yi taron kamu a rana ta biyu), da dina a wani ɗakin taro da ke Titin Minjibir duk a garin Kano, a rana ta uku.

To amma angon bai halarci ko ɗaya cikin shagulgulan bikin ba.
Hasali ma dai amaryar ba ta kai ga tarewa ba ya sake ta, wanda hakan ya zama abin takaici da ban-mamaki matuƙa.

Tun daga lokacin kuwa Sadiya ba ta ƙara shiga harkar fim ba, kuma ba ta samu yin wani auren ba.

Allah Ya jiƙan Alh. Abubakar, Ya yafe masa kurakuran sa, amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: