Friday, 16 February 2018
So Hana Ganin Laifi: hamshakin Mai Kudi Ya Zama kirista Sannan Ya Auri Diyar Osinbajo

Home So Hana Ganin Laifi: hamshakin Mai Kudi Ya Zama kirista Sannan Ya Auri Diyar Osinbajo
 Hamshakin mai kudi ya zama Kirista sannan ya auri diyar Osinbajo

Diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo mai suna Oluwadamilola Osinbajo

Yanzu kuma an gano cewa Kirista ne da yake aiki a cocin Redeemed Christian Church of God

Sabbin bayanai masu daure kai na cigaba da bayyana a zagaye da auren nan da ake sa ran daurawa a tsakanin diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo mai suna Oluwadamilola Osinbajo ko kuma Kiki da angon ta mai suna Oluseun Bakare da ke zama da ga hamshakiyar mai kudin na Bola Shagaya.


Kamar yadda muke samu daga majiyoyin mu, a sabanin yadda labarin ya fara fita na cewa wanda zai aure diyar ta Osinbajo musulmi ne, yanzu kuma an gano cewa Kirista ne da yake aiki a cocin Redeemed Christian Church of God.

ma'auratan ma sun hadu ne a majami'ar wajen ibada kafin daga bisanin soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su kuma har ma maganar aure ta shiga.

Wannan ne ma ya sanya mutane da dama ke ganin cewa wanda ke shirin angwancewar musulmi ne a da kafin daga baya a zama Kirista har kuma ma ta amince ta aure shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: