Saturday, 10 February 2018
S U L H U A L K A I R I NE! Abubuwan Da Sunka Jawo cece ku ce a Tsakanin Jaruman Biyu inji Falalu Dorayi

Home S U L H U A L K A I R I NE! Abubuwan Da Sunka Jawo cece ku ce a Tsakanin Jaruman Biyu inji Falalu Dorayi


Idan sulhu ya tabbata tsakanin mutum biyu. Ba dai dai bane a koma gefe ana jifan juna da maganganu. Hakan yana nuna ba'a girmama sulhu ba. Kuma hakan kara haifar da sabuwar fitina ne.. Mai tada fitina kuwa Allah ya la'ance shi.
Lallai girmama sulhu shine kusantar juna cikin Mu'amala, ku ringa tuntubar juna, kai ziyara gidajen juna, kiran waya domin tautaunawa ko zumunci. Ku nuna farin ciki akan shaaninku na alkairi, kuma kuyi tarayya cikin abin bakin ciki in ya samu dayanku. Wannan shine zai bayyanawa MASOYANKU tare kuke, kuma zaku magance GULMA da MUNAFUNCIN dake faruwa tsakaninku.
Wallhi Wallhi Wallhi
Muddin kuka koma gefe, kuka nuna ba ruwanku da juna, kun barwa SHAIDAN da masu ZUGA dama suna saka SHARRI a tsakaninku. Ku sani dukkanku kun fada ramin HALAKA mai girman gaske. Allah ya tsaremu.

Ubangiji yace "Kada kuyi Jayayya domin zakuyi rauni ku karye, karfinku ya tafi, ku zamto marasa kwarjini.

Ba abin da Jayayya tsakanin MADAUKAKA biyu take haifarwa face.
-Rabuwar kawuna.
-Fito na Fito da Juna.
-Cin mutunci da tozarci.
Lallai ba gazawa bace yafewa juna, in kaji a zuciyarka kafi karfin kai laifi ka nemi afuwa.
To SHAIDAN ya gama da kai.

Hakuri na daya daga cikin abin da zai bawa MUTUM tabbata akan gaskiya. {No good is there in much of their private conversation, except for those who enjoin charity or that which is right or conciliation between people. And whoever does that seeking means to the approval of Allah – then We are going to give him a great reward.}

Share this


Author: verified_user

0 Comments: