Tuesday, 6 February 2018
Ni ba da Ali Nuhu nake Rigima, da gurbatatun yan Kannywood Nake - Inji Adam A Zango

Home Ni ba da Ali Nuhu nake Rigima, da gurbatatun yan Kannywood Nake - Inji Adam A Zango
Fitaccen jarumin fina-finai hausa kuma mawaki Adam A.Zango ya bayyana cewa shi ba da abokin aikin shi Ali Nuhu yake rigima kamar yadda wasu ke zato.

Jarumin wanda ke cin gashin sabon shirin fim da ya fitar kwanan baya mai take "Gwaska Returns" » yana mai koke wajen kwato hakkin sauran abokan aikin sa.

Kamar yadda ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta » jarumin ya mayar da akalar fushin sa ga gurbatatun yan kannywood masu ruwa da tsaki game da miyagun ayyukan da suke yi na rashin adalci da bayar da cikakakken hakkin jama' a.

"Ni ba da Ali Nuhu Nike rigima ba. Da gurbatatun yan Kannywood nike rigima, wadanda basu da yardar Allah. Wadanda sai Ali Nuhu da Adam A.Zango kadai suke iya sakawa a fim. Wadanda suke danne hakkin iyayen mu jarumai idan suka saka su a fim. Wadanda suke danne hakkin kananan jarumai da crew, kuma su hana su magana. su kuma su kasa magana saboda kar gobe suki kiransu aiki.
Wadanda suka zabi adadin mutanen da zasu yi aiki dasu bayan kowa ya shigo neman abinci ne.
wadanda suka mayar da budget din fim N500,000 har a yi a gama kuma da manyan jarumai maza da mata.
Wadanda suke karbo kudi masu yawa daga sabbin furodusoshi daga waje kuma su cucesu. Ya rabuta a shafin sa na kafar sada zumunta.
Kan wannan babatun da yayi game da abubuwan bacin rai dake aukuwa a masana'antar, Jarumin ya ikirari cewa ana iya neman halaka shi amma shi dai ya sadaukar da ran wajen neman hakkin abokan aikin shi".

" Na sani ba lalle bane in zauna lafiya ba. Kuma na sani ana iya neman rayuwata amma duk da haka na bayar da raina".

Adam Zango yayi kira ga sauran abokan aikin sa da su rungumi sabuwar akida wanda ya kafa mai take "Tafiyar Gyaran Karaya"
Yace kofa a bude yake ga masu neman hada hannu wajen neman hakkin su domin a yan zu shi kadai ne a cikinta.

Wasikar da ya fitar kwanan baya
Wannan ba shi bana karo na farko da jarumin zai nuna facin ran sa game da abubuwa dake faruwa a masana' antar tasu. A kwannan baya ya fitar da budaddiyar wasika zuwa ga mahassadan » shi masu neman bata sunanshi a masana' antar shi.

Bugu da kari jarumun yace zai saka wando daya da duk wanda ke neman yi masa kazafi » .
Jarumin 'Gwaska' ya fitar da fushin sa a shafin sa na kafar sadarwa ta instagram inda ya kira kansa da damisa kuma wanda ya nemi shi da fada ba ya neman zaman lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: