Saturday, 10 February 2018
Nasan masu tayar da fitina a masana'antar fim din Hausa kuma idan suka sake zan tona musu asiri - Inji Ali Artwork

Home Nasan masu tayar da fitina a masana'antar fim din Hausa kuma idan suka sake zan tona musu asiri - Inji Ali Artwork

Tauraron me wasan barkwanci na fina-finan Hausa, Ali Artwork ya sake yin magana akan rikice-rikicen dake faruwa a masana'antar fina-finan Hausa, inda yace yasan masu tayar da fititinar su noke. Ali yace nan gaba idan aka sake ta da wata fitina zai fito ya bayyana sunan ko wanene ya haddasata domin baya tsoron kowa.

A satin daya gabatane dai aka samu fadan cacar baki tsakanin masoyan Ali Nuhu da Adam A. Zango inda har saida takai hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta shigo ciki ta sasanta tsakaninsu domin abin yana nema ya wuce yanda ake tsammani.

Tun a wancan lokacin Ali Artwork ya bayyana cewa jaruman biyu, Ali Nuhu da Adam A. Zango ne suke hada fadan da gangan dan kawai su gwara kawunan masoyansu:

Ga sabon sakon na Ali Artwork kamar haka:

"Salam Yan uwa da abokan arzikin Ina so in amfani da wannan da ma inja hankalin yan KANNYWOOD akan su guji tada fitina da raba kan masoyansu dan Allah ya tsinewa mai tada ita kuma mu munsan suwaye ke tada ta su noke dan haka kusani ba zamu taba biyayya GA masu saba dokar Allah ba idan wani ya kara tada fitina to kusani zamu fito mu fadawa duniya mutane da suke tada wa saboda wata mummunar manifarsu wanda mutane basu san da hakan ba wallahi ni Ali Artwork ba butulu bane kuma bantaba butulci ba sannan kuma ni ba marar kunya bane ni mai fadar gaskiyane komai dacinta dan bana tsoro kowa face mahaliccina Allah saboda nasan cewa mutum bashi da wuta bashi da aljannah duk wanda kaga ina mu'amala dashi kaga mun rabu to dabi'unsa ya sabawa dokar Allah ni kuma banga dalilin da zaisa in bar Allah in bika ba babu wani wanda nake bi da sharri sai dai alkhari kuma ba wanda ya Isa in masa kazafi duk abunda kuka GA na fada iya gaskiya ta nake fada ba dan son rai na ba kuma mu munsa wa yanda suke haddasa fitintinu a masana'antar KANNYWOOD saboda ana basu dama suna kawo GULMA da MUNAFURCI tun a shekarun baya munyi iya bakin kokarinmu don ganin an kawar da irin wannan gurbatattun mutane daga masana'antar amma abun ya faskar daga kashe muka ga abun bamai gyaruwa bane saboda yan fada yau in baka kawo gulma da munafurci to kai bakomai bane shiyasa ni Ali Artwork kuka ga na koma gefe

#Ina_Kallonsu_kyar don haka kusani duk wanda ya sake tayar mana da fitina zamu sa kafar wando daya da mutum zamu dauko alkalamin mu muyita rubutu a kan mutum har sai duniya ta gane gaskiyar damuke fada a kan mutum insha Allah"

Share this


Author: verified_user

0 Comments: